Babban mai koyar da ‘yan wasan Golden Eaglets na Najeriya, Emmanuel Amuneke, yace sauye-sauyen da yayi a bayan da aka komo daga hutun rabin lokaci, sune dalilan da suka sanya Najeriya ta samu nasarar lashe kofin duniya ta samari ‘yan kasa da shekara 17 a kan kasar Mali.
‘Yan Golden Eaglets sun doke Mali, wadanda sune ke rike da kofin zakarun Afirka, da ci biyu da babu a wasan karshe, suka amshi wannan kofi na duniya a karo na biyar a tarihin gasar.
Amuneke yace sun yi kokarin kawar da kura-kuran da ‘yan wasan ke tabkawa, musamman ma a aunin farko kafin zuwa hutun rabin lokaci, inda ‘yan Najeriya suka yi ta hasarar kwallon a tsakiyar fili. "Ba na son in yi korafi sosai saboda yara ne. Mun sauya wasu abubuwan da muke yi cikin filin da aka komo daga hutun rabin lokaci, sannan muka sauya wasu ‘yan wasa. Wannan ya kara karfin wasanmu" in ji shi.
Amuneke ya bayyana farin cikinsa da ganin yadda kwazon yaran ya kai su ga samun nasara, tare da yabawa irin goyon bayan da suka samu.
Mai koyar da ‘yan wasan kasar Mali, Baye Ba, yace shi ma yana alfahari da bajimtar ‘yan wasansa a gasar cin kofin duniyar da aka kammala a Chile, yana mai fadin cewa da ma ‘yan Najeriya ba kanwar lasa ba ne.
"Wannan shi ne karon farko da Mali take kaiwa ga wasan karshe. Idan kayi Imani da cewa kana iya lashe wani wasa, to dole ranka ya baci idan aka doke ka. Amma duk da haka ina alfahari, domin ba kowa ne ya kai ga matsayin na biyu ba" in ji kwach na ‘yan wasan Mali.