Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Najeriya Zasu Kara Da Burkina Faso A Congo


Wani mutum yana nuni da hannunsa cikin Filin Wasan Kwallo na Kasa yayin da daruruwan masu neman aiki ke rubuta jarabawar fitar da kwararru a Abuja 15 ga watan Maris shekarar 2014.
Wani mutum yana nuni da hannunsa cikin Filin Wasan Kwallo na Kasa yayin da daruruwan masu neman aiki ke rubuta jarabawar fitar da kwararru a Abuja 15 ga watan Maris shekarar 2014.

Kungiyar matasa ‘yan wasan kwallon Najeriya, ‘yan ‘kasa da shekaru ashirin ashirin da uku wato U-23, zasu kara da Burkan Faso a wasan kusa da karshe na wasannin da ake a kasar Congo, bayan sa’ar da matasan Najeriya suka samu a lokacin wasan su da kasar Sudan a jiya Litinin, inda aka tashi kunnen doki.

A daya bangaren kuma na wasan kusa da karshe, masu masaukin baki wato kasar Congo zata kara da Senegal.

Matasan dai sun lallasa kasar Ghana da ci biyu da nema a wasan farko na rukunin su, amma sun sunyi kunnen doki da kasar Senegal a wasan rukununsu na karshe.

Ibrahima Keita dai shine ya dora Senegal gaban Najeriya mintuna 82 a wasan inda ya zarga kwallo raga, amma Mustapha Abudullahi ne ya farke kwallon mintuna bakwai bayan da Ibrahima ya jefa kwallon raga.

Sakamakon wasan ne dai yasa matasan ‘yan Najeriya suka zamanto kungiyar farko a rukunin su na B, haka kuma na nufin sun kaucewa haduwa masu karbar baki wato kasar Congo.

Ana ganin kungiya ta Samson Siasia na daga cikin kungiyoyi masu kyau a gasar, ana kuma ganin ‘yan wasan Burkina Faso ba zasu zama barazana ba ga ‘yan Najeriya.

XS
SM
MD
LG