A wani yunkuri na kwato garin Mubi dake hannun ‘yan bindiga masu tada kayar baya na kungiyar Boko Haram, shedun gani da ido dai sunce sunga ‘yan sandan kwantar da tarzoma wato mobile police na kutsa kai akokarin zuwa kwato garin na Mubi.
Tabakin wasu shedun ido sunce, tawagar ‘yan sandan kwantar da tarzoma wato ‘yan sandan MOPOL sun wuce cikin shiri, harma sun wuce inda sojoji suke sunma kai har kasuwar dare inda akace sojojin Najeriya ma basu iya zuwa, mutane dai sun yabawa ‘yan sandan kwantar da tarzomar kan kokarinsu na wannan yunkurin.
Shin me al’ummar yankin ke bukatane daga jami’an tsaron, Mallam Ahmed Sajo wani dan asalin yankin Mubi’n ne yace, “da dai za’ayiwa garin ‘kawanyane azo a samesu a fitar dasu daga garin, a karbe mana garinmu a maida mana hannun mu, mu abinda muke roko kenan da kuma fatanmu.”
Ya zuwa yanzu dai ‘yan kungiyar ta Boko Haram na cigaba da aiwatar da tsarin shari’ar su inda ma har suka aurar da ‘yan mata dakuma wasu matan da mazansu suka gudu. Saurari cikakken rohoton Ibrahim Abdul’aziz.