Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yanzu Kasar Brazil Ce Ta Daya A Faggen Wasan Kwallon Kafa A Duniya


Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya watau Super Eagles, yanzu tana mataiki na biyar a faggen wasan kwallon kafa a nahiyar Afirka, wannan na kunshe ne a cikin sanarwar hukumar kwallon kafa ta duniya na wanda ke fita kowane wata.

Sanarwar ta kara da cewa a duniya kuwa Najeriya tana matsayi na araba’in (40).

Kasashen dake gaba da Najeriya a Afirka sun hada da Eygpt, Senegal, Cameroon da Burkina Faso.

Cameroon wacce zata kara da Najeriya, a wasan neman gurbi buga wasan cin kofin kwallon kafa na duniya na 2018, itace ta talatin da uku (33) a duniya kuma ta uku, a nahiyar Afirka.

Brazil, ta komo ta daya a duniya yanzu tun bayan da matsayin ya kubce mata kimanin shekaru bakwai da suka wuce.

Fidda Brazil da aka yi daga gasar cin kwallon kafa da aka gudanar a kasar Afirka ta kudu a shekarar 2010, she ya sata samu koma baya a wacan lokacin a yanzu Argentina ce ta biyu sai kasar Jamus a mataki na uku ita kuwa kasar Chile tana ta hudu san nan Colombia tana ta biyar.

XS
SM
MD
LG