‘Yan sandan jihar Ohio sunce wani ‘dan makarantar firamare ya saci kudi dala dubu ashirin da biyar kimanin Naira miliyan biyar, daga wurin kakan sa daga baya ya fara rabon dala ‘dari ‘dari ga ‘yan ajinsu.
Hukumomi sunce yaron ‘dan shekaru goma sha uku da haihuwa ya rabar da dubban daloli a wannan satin kafin jami’an makarantar suka Ankara da abinda ke faruwa.
Masu bincike kan lamarin a garin Medina dake arewa maso gabashin jihar Ohio, sunce a yanzu haka sun sami karbo dala dubu bakwai kacal daga cikin kudin.
‘Yan sanda sun gayawa jaridar garin Medina gazzette suna kokarin gano yadda yaron ya saci kudin daga gurin kakansa ‘dan shekaru tamanin da uku. Sun kuma ce za’a yi garaje ga dami, sani ko za’a caji yaron.
Malaman makarantar dai sun sami labarin rabon kudin a ranar Laraba, amma a wannan lokacin ‘yan sanda sunce wasu sun riga sun kashe kudin.