Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawan Attajirai Zai Karu a Najeriya Nan da Shekaru Hudu - In ji Wata Kungiya - 04/03/14


Kungiyar ta ce yawan 'yan Najeriya da zasu iya kashe Dala Miliyan daya zasu karu da kusan kashi hamsin cikin 100 a shekaru hudu masu zuwa.

Yawan attajirai zai karu a najeriya da kashi arabain da bakwai a cikin shekaru hudu masu zuwa domin karuwar darajen gidaje da hannayen jari a yankin Afirka ta yamma,inji kungiwar dake kula da labaran attajiran duniya.

Kungiwar tace yawan 'yan Najeriya da zasu iya kashe dala miliyan daya kai tsaye zasu karu zuwa mutane dubu ashirin da uku a cikin shekaru hudu.

Kungiyar dake kula da labaran attajirai na duniya wanda ke Afirka ta kudu ne ta bayyana haka a cikin wata kasida a yau, inda ta kara da cewa kashi ashirin da shida na jimilar kudaden wadanna attajiran dala biliyan tamanin da biyu su na bankunan kasashen waje.

A wani labarin kuma, Kimani Naira biliyan dari da gwamnatin taraiya ta kashe domin farfado da masaku a Najeriya da alamun cewa kudaden sunbi ruwa .

Shugaban kungiyar yan kasuwa da masana'antu Mohammed Abubakar, yace idan har za'a raya masaku dole ne ayi tanajin yanda sa'a sami audoga da kuma ganin cewa an tanaji naurorin zamani a masakun da zasuyi gogaiya da na duniya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:00 0:00
Direct link
XS
SM
MD
LG