Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Gudanar Da Wasanni Na Kasashen Musulmi Na Duniya


 Ben Nunoo Mensah
Ben Nunoo Mensah

Shugaban hukumar Olympic na Ghana Mr Ben Nunoo Mensah ya gana da babban limamin Ghana Sheikh Usman Nuhu Sharubutu don tattaunawa a kan yanda Ghana zata shiga gasar wasannin hadin kan Musulmi ta duniya a karo na farko da aka shirya yi a Istanbul na kasar Turkiya a shekarar 2021.

Ya zuwa yanzu, hukumar Olympic na Ghana da al’ummar Musulmin Ghana karkashin jagorancin babban limamin kasa, sun amince da shirya takardu da zai ba Ghana daman zama mamba na hukumar wasannin hadin kan Musulmi na duniya, ta ISSF wacce take shirya gasar.

Wannan batu ya bayyana ne a lokacin da Mr Nunoo ya kaiwa Sheikh Usman Nuhu Sharubutu ziyara a gidansa. Gasar wasannin hadin kan Musulmi ta duniya, ta tara kasashe da dama da kuma fannonin wasanni iri iri da ita hukumar ISSF take shiryawa, dake hada ‘yan wasannin guje guje da tsalle tsalle daga kungiyar kasashen Musulmi na duniya wanda a halin yanzu take da mambobi 57.

A wannan gasar ana bada dama ga wadanda ba Musulmi daga wadannan kasashe mambobi shiga wasannin, wanda aka fara shiryawa a shekarar 2005 a Saudi Arabia.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:10 0:00

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:10 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG