Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Inganta Aiyukan Horar Da Matasa Sana’oi Domin Dogaro Da Kai


Gidauniyar koyon sana’oi a Najeriya watau Industrial Training Fund, ko kuma ITF, tace zata inganta aiyukan horar da matasa da sana’oi domin dogaro da kai da bunkasa tattalin arzikin kasa.

Gidauniyar ITF, an kafata ne fiye da shekaru arba’in da suka gabata, bayan Turawan milkin mallaka sun fara barin kasar domin a samu ‘yan kasa da zasu cike guraben da Turawan suka bari musamman a masana’antu.

Darakta janar, na hukumar ta ITF, Joseph Ari, ya ce mafi yawan kasashen duniya, da suka ci gaba sun dukufa ne wajan sana’oi, da inganta masana’antun su.

Ya kara da cewa zaka ga mutun a Najeriya, yana da digiri fiye da daya amma inda ka bashi aikin hannu bazai iya ba yana mai cewa wanna yana kawo koma baya ga kasa.

Kawo yanzu dai gidauniyar ta horar da mutane fiye da miliyan goma sha takwas in ji daraktan kula da shiga da fitar kudi Aliyu Ahmed Kyari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

XS
SM
MD
LG