WASHINGTON, DC —
Shugaban Cibiyar Kiyaye Barkewar Annoba da yaki da Cututtuka a nan Amurka yace yana da karfin gwiwar cewa za’a iya kawo karshen annobar Ebola a yammacin Afirka.
Da yake magana da jami’an kiwon lafiya da kuma ‘yan majalisar dokokin kasa jiya Talata a nan birnin Washington, Dr. Tom Frieden yace nan gaba fa za’a tashi babu cutar ko daya a duk fadin duniya, idan aka cigaba da tafiya akan turbar da ake a halin yanzu.