A cigaba da bayyana ra’ayoyinsu da matasa ke yi game da makomar zaben Nijeriya, Comrade Abdulmajid Babangida Sa’ad, wakilin hadakar kungiyar wanzar da zaman lafiya ta matasan Musulmi da Kirista “Muslim and Christian Youths Foundation for Peace and Unity” a yankin Arewa maso yammacin Najeriya ya ce taron da su ka yi a Kano ya biyo bayan rade-radin da ake bazawa cewa da yiwuwar a sake dage zabe.
Ya ce sun yi amfani da taron wajen kwantar ma matasa hankali da kuma sake jaddada muhimmancin daukar duk wani mataki ta hanyar da ta dace. Ya ce sun lura cewa matasa da daman a cikin bacin rai saboda dage zaben da aka yi.
Ya ce baya ga kwantar wa matasa rai, sun kuma dubi hanyoyin da za su tabbatar da zaman lafiya a Nijeriya. Comrade Abdulmajid ya gaya wa wakiliyarmu Baraka cewa matasan sun kuma lura cewa ita kanta gwamnati ma akwai rawar da za ta taka ta tabbatar da zaman lafiya a kasa, kuma rashin sake dage zaben na daga ciki.