Ana Jin karar Harbe-Harbe Cikin Daren Nan A Potiskum

Potiskum, Nigeria

A wani lamarin da har yanzu babu tabbas kan ko menene ke faruwa, ana ta jin karar harbe-harben bindigogi a Potiskum dake Jihar Yobe.

Mazauna garin na Potiskum sun ce an fara jin karar harbe-harben tun wajen karfe 8 da wani abu na wannan daren alhamis, da farko jefi-jefi, amma daga baya aka goce sosai da harbe-harbe.

An ce karar harbe-harben na fitowa ne daga inda ofishin 'yan sanda na yanki yake a kusa da gidan waya na tsakiyar garin Potiskum.

Wani mazaunin Potiskum, Alhaji Muntari Adamu Yerima, ya fada mana yanzun nan cewa babu karar fashe-fashen bam ko nakiya, amma harbe-harben yayi tsanani kuma mutane sun gudu zuwa cikin gidajensu.

Har yanzu dai babu wani bayani na ko menene ke faruwa. A cikin kwanaki biyun nan dai, an samu tashin bama-bamai da dama a garin na Potiskum, dukkansu a kan cibiyar Musulmi ko Masallaci.

Your browser doesn’t support HTML5

Alhaji Mukhtar Adamu Yerima Yana Bayanin Harbe-Harben Da Ake Yi A Potiskum 2'33"