Na Fara Da Snooker, Yanzu Har Kamfanin Yin Ruwa Nake Da Shi in ji Wani Matashi

Gasar Snooker Ta Kasashen Turai

Wani matashi mai suna Tijjani Ado Ahmed dake Kano a arewacin Najeriya, yace kishin kansa, da kuma gujewa bin mutane yana roko suka sanya shi ya fara sana'ar Snooker, har ta kai yanzu yana da kamfanoni da yawa.

Malam Tijjani yace ya fara Snooker da karamar teburi, har yazo ya sayi babba, yayin da a yanzu yake da kamfanonin sadarwa da na sarrafa ruwan sha.

Matashin yace a yanzu haka akwai mutane kusan 30 wadanda suke aiki kai tsaye a karkashinsa, duk a saboda kudurin da yayi tun farko cewa ba zai kaskantar da kansa yana bin mutane yana roko ba.

Matashi Tijjani yace yayi makarantar firamare ne kawai, amma kuma yana da niyyar neman hanyar da zai kara ilminsa.

Your browser doesn’t support HTML5

Daga Sana'ar Snooker Yanzu Ina Da Kamfanoni Da Yawa - 2'05"