Wani malamin makarantar sakandaren kimiyya ta Potiskum, yayi bayanin yadda wani dan harin kunar bakin wake ya kashe kansa tare da dalibai masu yawan gaske a lokacin da dalibai ke taruwa da safe kafin shiga ajujuwansu.
Malamin yace wannan dan harin, yayi shiga kamar dalibi, dauke da wata jaka a bayansa kamar dai dan makarantar. Amma sauran dalibai sun fara shakkar aniyarsa a lokacin da aka fahimci yana ta kokarin shiga tsakiyar daliban ne.
Yace dalibai da dama sun fara daga murya game da wannan dan harin da tun farko aka dauka cewa sabon dalibi ne a makarantar, kuma ganin an fara sanya masa ido da magana ne sai yayi wuf ya tayar da bam din dake kunshe a bayansa.
Yace bam din ya raba kan wannan mahari da gangar jikinsa.
A saurari cikakken bayaninsa.
Your browser doesn’t support HTML5