WASHINGTON, DC —
Wani tsohon dan majalisar wakilan tarayya daga Jihar Borno, Dr. Haruna Yerima, ya fadawa Muryar Amurka cewa zasu gurfanar da babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, muddin bai fito ya bayyana wa duniya dalilai masu gamsarwa na irin sojoji da makaman yakin da ake bayarwa kariya ga tsohon gwamnan Borno, Modu Ali Sheriff ba.
Dr. Yerima yace idan domin shi tsohon gwamna ne, akwai tsoffin gwamnoni uku a Borno wadanda suke tafiya cikin mota babu mai gadi ko guda daya.
ya kuma ce me yasa sai da shi Ali Modu Sheriff ya koma jam'iyya mai mulki ta PDP sai aka fara yi masa wannan gatanci na sojoji masu dan karen yawa, tsaron da ko shi gwamnan Borno na yanzu, Kashim Shettima, ba a ba shi?
Your browser doesn’t support HTML5