Gwamnatin Amurka, ta bayyana takaicin matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka na soke horaswar da Amurka ta ke bayarwa ga wata bataliyar sojojin Najeriya.
A tsakanin watan Afrilu da Agusta na wannan shekara, Amurka ta gudanar da horaswa har sau biyu. An shirya gudanar da horaswa ta uku da niyyar shirya wannan bataliya ta yadda sojojinta zasu mallaki dabarun yaki na zamani masu inganci.
Wata sanarwar da ofishin jakadncin Najeriya dake Abuja ya bayar, ta ce Amurka tana takaicin soke wannan shirin ana tsakiyarsa, domin shi ne na farko a wani shirin horas da sojojin Najeriya da nufin samar musu da irin dabaru masu nagarta da zasu iya yakar kungiyar Boko Haram.
Sanarwar ta ce Amurka zata ci gaba da aiki da sauran sassan dangantakar tsaro mai yawa dake tsakanin kasashen biyu, da wasu ayyukan tallafin da ta saba bayarwa ga Najeriya.