An Haifi Jaririya Da Tagwaye A Cikinta

An haifi wata jaririya a Hong Kong dauke da cikin tagwaye, amma kuma ‘yan’uwanta ne a bias cewar likitoci.

Irin wannan al’amari, wanda ake kira “Fetus-in-Fetu” a kimiyyance, ba abu ne da ya saba faruwa ba, amma a kan samu irinsa sau daya cikin haihuwa rabin miliyan daya. Har yanzu masana bas u da tabbas kan abinda ke haddasa shi.

Dr. Draion Burch, likitan cituttukan mata a Pittsburgh dake Jihar ennsylvania a Amurjka, y ace wasu abubuwa na ba-zata sukan faru a daidai lokacin da mace ta samu ciki, amma bamu fahimce sub a sosai. Wannan yana daya daga cikinsu in ji shi.

Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya tana daukar dan tayin da aka samu a cikin jariri ko jaririya a zaman wata irin sankara da ake kira Teratoma.

Amma likitocin da suka duba wannan yarinya sun ce wadannan ‘yan tayi biyu da aka samu a cikinta, ba sankara ba ce, abinda ya rage ne na ‘yan tayi guda biyu da jikinta ya tsotse a lokacin da uwarsu ke da ciki. Suk ace a bias dukkan alamu, da farko cikin ‘yan uku ita wannan uwa tasu ta yi.

Da farko an kai wannan jaririya ce ga wani likitan mata mai suna Dr. Yu Kaio-man na asibitin Queen Elizabeth dake Hong Kong a saboda ana tsammanin tana da sankara a cikinta.

A lokacin da uwar take da ciki, hotunan Ultrasound da aka dauka sun nuna akwai wani abu a cikin jaririyar, amma ba a san ko menene ba.

A lokacin da jaririyar ta cika makonni uku da haihuwa, an yi mata tiyata, a lokacin da aka gano wasu ‘yan tayi guda biyu, a dunkule a tsakanin hanta da kuma kodarta.

Daya daga cikin ‘yan tayin na da nauyin gram 9.3, daya kuma gram 14.2, wanda ke nuna cewa daya yayi mako 8, daya kuma mako 10.

Kowanne daga cikin ‘yan tayin da aka samu a cikin ita wan nan jaririya na da cibiyar dake hade da wani abu mai kamar mahaifa a cikin tumbin ita wannan jaririya.

Likitoci suka ce jaririyar ba ta kai inda za a ce ta yi cikinsu ba. A maimakon haka suka ce ita wannan jaririya da farko tana cikin ‘yan uku da uwar ta dauki cikinsu. A saboda wasu dalilan da ba a sani ba, sai kanana biyu daga cikin ‘yan tayin suka shiga cikin ‘yar tayi mafi girma.

An ga alamun cewa wadannan ‘yan tayi biyu sun a da ransu kuma sun a girma a lokacin da jikin ta farko ya tsotse su. Amma Dr. Burch yace a bayan shigarsu cikin ita dayar, sai suka kasa girma.

Dr. Burch yace sun a bukatar abincin dake shiga jikinsu daga cibiyar dake hada su da mahaifa, amma daga lokacin da suka rasa wannan, sai komai nasu ya tasaya cik.