Al’ummar garin Bournemouth dake bakin ruwa a kasar Ingila sun wayi gari cikin murna da mamakin cewa kungiyar kwallon kafar garinsu, AFC Bournemouth, wadda saura kiris a rushe ta baki daya shekaru 5 da suka shige, tana dab da shiga cikin rukunin manyan kulob-kulob na Ingila a wasannin Firimiya Lig.
Manajan Bournemouth, Eddie Howe, yace abin kamar mafarki, domin shekaru 6 da suka shige, wannan kulob ta durkushe, ba ta da komai, ba ta iya biyan ‘yan wasa ko ma’aikatanta. Magoya bayan kungiyar, sun yi ta ciro kudade a aljihunsu suna bayarwa gudumnawa. Gudumawar da shugaban kulob din, Jeff Mostyn ya bayar ta Fam dubu 750 daga aljihunsa ta taimaka wajen tabbatar da cewa ba a rushe kulob din ba.
Amma a yanzu, ganin cewa Bournemouth zata shiga sahun kungiyoyi irinsu Chelsea da Manchester United, a karon farko cikin shekaru 116 da kafa wannan kulob, ya janyo doki a wannan dan karamin gari. Filin wasa na Bournemouth yana daukar mutane dubu 12 ne kacal, kuma kwata kwata abinda take samu a shekara kimanin fam miliyan 5 ne. Amma a yanzu da zata shiga gasar Firimiya Lig, abinda zata samu, koda shekara daya tak ta yi, zai kai akalla Fam miliyan 120, abinda zai ba ta sukunin iya sayen ‘yan wasa masu kyau.