WASHINGTON, DC —
Mawakin Hausa na zamani, Andy Bature, yace babbar matsalar da take damun matasa a wannan zamani, ita ce ta mutuwar zuciya, wadda ke haddasa musu girman kai da kasalar kin rungumar wasu sana'o'i da yawa.
A cikin hirarsa da Dandalin VOA, Andy Bature, yace ya kamata matasa a arewacin Najeriya su tashi tsaye su rungumi kowace irin sana'ar da zata iya kawar da su daga dabi'ar yin maula da banga.
Yayi misali da yadda ya rungumi waka, wadda ta rufa masa asiri, har ma wasu na samu karkashinsa ko a dalilinsa.
Your browser doesn’t support HTML5