Rashin Miji Bai Zama Karshen Rayuwar Mata

Sana'ar Tuyawan Waina

Babban mahimanci ilimi ga rayuwar diya mace na da matukar mahimanci, idan akayi la’akari da yadda rayuwar yau da kullun ke gudana. A tabakin Malama Hauwa Aliyu, wadda ta kasance batayi ilimin zamani ba a lokacin kurucciyar ta, gashi kuma ta shiga cikin wani hali na rayuwa, wanda idan da kace tayi karatu, da yanzu da tasamu kanta a wannan halin da zata’iya taimakama kanta ta hanyoyi da dama, ta dai fara sana’a tane bayan rabuwar ta da mijin ta uban ‘yayanta.

Ta kasance tana fuskantar matsaloli a rayuwa wanda yakaita ga halin da tasamu kanta, yanzu tana sana’ar sayar da abinci, da wannan sana’ar take tallafawa kanta da ‘yayanta tana biya musu kudin makaranta, da duk sauran abubuwan rayuwa. Tana ganin wannan halin da tasamu kanta idan da ake tayi karatun zamani, to da yanzu sai dai kawai ta fara aiki.

Don haka tayi kira ga iyaye da su bar ‘yayansu su samu ilimin zamani don suyi dai daito da rayuwar yau da kullun. Kasancewar rayuwa a wannan zamanin tazama wani abu da kowa yakamata ya tashi tsaye wajen neman ma kanshi abun dogaro.