'Yan Dako na Tallafawa Tattalin Arzikin Kasa a Najeriya

'Yan dako

Babu tattalin arzikin kasa da kan zama wani abu batare da taimakon wata kasa ba. Amma abun la’akari dashi a nan shine, yakamata ace kowace kasa da ke tunkahon arziki, da kuma neman cigaba a tattalin arzikin kasar, sai sun maida hankali wajen inganta nasu masana’antun kamin ma su samu su zama wani abu.

Malam Adamu Zanna, dan dakone a kasuwar kwari ta jihar Kano, wanda yake magana a madadin ‘yan kungiyar tasu, dangane da wani yunkuri da gwamnati keyi na hana kasuwancin kasar China a ilahirin kasar. Suna ganin kamar wannan wani koma bayane ga tattalin arzikin kasar, kasancewar kusan duk daukacin kayan da ake amfani da su a kasar suna da nasaba da kasar China, a dalilin rashin tsayayar wutar lantarki, rashin hanyoyi nagartatu, ga kuma rashin wadatacen manfetur.

Duk irin wadannan suke haifar da koma baya ga tattalin arzikin kasa. Uwa uba maganar rashin aikinyi wata abuce da yakamata a lura dashi wanda wadannan kasashen suna taimakawa wajen samama matasa aikinyi, misali yanzu a nan jihar Kano, a kwai ‘yandako kimanin dubu dari uku, wanda kuma mafi akasarin su matasane, suna wannan aikin ne don inganta raruwarsu kasancewar gwamnati ta gaza wajen samar da aikinyi ga ‘yankasar.

A zahirin gaskia yakamata ace gwamnati ta maida hankali ne wajen karfafa masana’antu da tallafawa masu karamin karfi don a samu a dawo da karfin tatalin arzikin kasar, ba kawai su maida hankali wajen rage aikin yi ga matasa ba.