Ali Muhammad Yakasai, wani matashi ne mai saida kankara, ganin yanayi zafi da ake ciki yanzu a wannan wata na Azumi, sukan kulla wannan kankarar domin masu siya a sari ko dai-dai. Sukan taimaka ma sauran al’umah wajen samun saukin wajen sanyaya abubuwan sha lokacin budabaki.
Ta wannan sana’ar ta su sun sama ma matasa abunyi da dama, wanda taka wasu sunkansamu dammar taimakama ‘yan’uwansu. Matsalolin da kuma suke fuskanta baiwuce na rashin tsayayyiyar wutar lantarki ba. Amma dai suna iya kokarinsu wajen ganin sun yi maganin wannan matsalar a kowane lokaci.
Burinsu shine Allah yasa su cigajiyar wannan da kuma falala ta zuwa wasu wajaje, don al’umah su samu saukin gudanar da rayuwa bacikin wahala ba. Kana suna kara kira ga matasa da sutashi haikan wajen neman sana’ar yi kowace irice.