Babu Kaskantacciyar Sana'a ga Matasa

Matashi mai sana'ar Faci da sa Iska

Matasa kada ku rena sana’a kowace iri ce, domin kuwa ba ku san irin daukakar da Allah zai yi muku a cikin wannan sana’ar ba. Zaharadeen Adamu, wani matashi ne mai shekaru goma sha tara, wanda yake kasuwancin faci da sa iska, a motoci, mashina, da ma keke.

Ya koyi wannan sana’ar a wajen mahaifinsa tun bayan kammala karatunsa na Firamari, a cikin wannan sana’ar har ya samu zuwa makarantar Sakandire ya kamala, ya kuma bayyanar da cewar wannan sana’ar tasa yanasamu kwanciyar hankali, da natsuwa, yana kuma yin lalulorirnsa duk a cikin wannan sana’ar. Yana da kuma burin ya daukaka wannan sana’ar zuwa wani mataki na zamanance.

Babban kiranshi ga matasa ‘yan uwanshi shine su dukufa wajen neman na kansu batare da zabe wajen sana’a ba, sukuma sani dacewar sana’ar hannu itace abu da yafi kamata ace kowane matashi ya iya, domin kuwa zai iya dogaro da kanshi a kowane lokaci. Kana kuma su kokarta su koma makaranta don dai daito da zamani. Yakan dai fuskanci wasu kalubale, wanda a lokutta da dama idan yayima mutane faci sai bayan ya gama sai su bashi naira talatin ko arba'in suce mishi yayi hakuri, amma abunda ake karba shine naira hamsin, a irin wannan halin yakan karba domin yana kokarin ya taimaka ne ba kawai yasamu kudinba shine burinshi.