Sirrin Cin Jarabawar WAEC Da NECO Ga Matasan Najeriya

Yan makaranta

Sanin kowa ne cewar Ilimi shi ne gishirin zaman duniya. Duk wanda ya kasan ce bashi da ilimin zamani, to ba shakka zai iya yin dana sani a rayuwarshi. A shekarar bana, rahotanni da su kayi nuni da cewar kimanin kashi 62% na dalibai, da suka zauna jarabawar kamala makarantar sakandire, sun fadi jara bawa. Mrs. Makama Audu, malama ce a makarantar sakandiren Capital School da ke Kaduna.

Tace mafi akasarin yara basa maida hankali wajen darasi da ake koyar da su, a yayin da malami ke gabatar da darasi, a sau da yawa, yara kan yi tunaninsu a kan wasu abubuwa na rayuwa. Kuma da yawa yara kan mai da hankali wajen soyaya, musam ma idan makarantar aka ce yara na hade da mata da maza. Wani abu da yara yanzu suka dauka wanda shima yake sa hankalin yara kan fita a lokacin darasi a aji shine, yadda yara kanyi amfani da wayar hannu a makarantu, shi ma wanna wata babbar matsala ce da take shafar karatun yara.

A bangaren iyaye kuwa, mafi akasarin iyaye basa nuna ma yaransu mahimancin karatu, sukan kawai sasu makaranta su kuma tilasta su da sai sunje, wanda babban abun da yakama ta ace sun yi shine su fahimtar dasu matukar mahimancin karatun, da nuna musu cewar da wanna karatun kawai zasu iya zama wani abu a rayuwa, idan suka maida hankali sukayi.

Sai itama gwamnati yakamata ta kokarta wajen sama ma dalibai wajen karatu mai nagarta, da kuma samar da kayan aiki. Kana wani babban muhimin abu da yakamata ace gwamnati ta maida hankali akai shine, wajen daukan malamai yakamata a tabbatar an dauki wadanda suka kware, a fannin koyarwa ba kawai a dauki wadanda suka san wasu ba, ko suke da wata digiri wanda take bata bangaren koyarwa ba.

A karshe kuwa yakamata malamai su maida hankali wajen ganin sun rike, amanar da aka basu wajen koyar da yara bisa gaskia. Kuma duk wanda bai karanci bangaren koyarwa ba, to kada a bashi aikin koyarwa har sai yasamu wani horaswa na musamman a bangaren ilimin yara.