Rashin Tauna Magana A Shafin Yanar Gizo Kan Dauki Rayuwa

Monica Foy

A wannan zamanin karni na 21 kowane abu yana da amfani da rashin amfanin sa. Musamman ma idan akayi la’akari da yadda matasa ke gudanar da rayuwar su, babban abun dubawa a nan shine, wai taya matasa ke cin gajiyar wanna kafa ta yanar gizo?

Illolin shafufukan yanar gizo na da yawa, wata daliba mai suna Monica Foy, a jami’ar jiha ta Sam Houston, ta dauko bana ba gammo. Domin kuwa ta shiga shafin ta na tweeter, inda ta yi wani rubutu da yanzu haka yasa ta cikin hadari, wanda hakan kan iya zama sanadiyar sadaukar da rayuwarta baki daya.

A ‘yan kwanakin baya ne a kasamu rahoton mutuwan wani jami’in ‘yan sanda, wanda aka kashe shi kuma ba’a san wadanda suka aikita wanna aikin ba, ana cikin haka sai wanna matashiyar, ta rubuta a shafin ta na tweeter, da cewar "wai meyasa mutane ke damuwa da mutuwar wanna jami’an ‘yansandan? Koma dai mutane sun san abunda yasa aka kashe shi? Ai kila ya chan-chan-chi a kashe shin! Kuma yana da wani irin Ido!"

Wadanna kalaman na wanna yarinyar ya jawo hankalin hukumomi, wanda ake tambayar me yasa tayi wadannan munanan kalaman ga wanna mamacin. A yanzu dai haka tana tsare a hannun hukumomi ana kuma yimata tambayoyi, wanda daga bisani za’a gurfanar da ita agaban kuliya. Wannan kan iya zama sanadiyar rasa rayuwar ta, don haka matasa su san mai zasu dinga rubutawa a shafufukan su na yanar gizo.