Da Tsohuwar Zuma Ake Magani Matasa

Soyayyar kuruciya itace soyayya, bata kan hanya ba. A duk dare idan muna kan teburin cin abinci nakan kalli gefe na, sai naga mijina kuma nakan tuna cewar tun muna ‘yan makarantar sakandire muke soyyaya.

Ashe kuwa duk wadanda sukayi soyyayya tun da kuru ciyar su, su kan samu wata kyakyawar fahimta fiye da ace an fara soyayya da girma. Shekarun mu 17 muna soyayya kamin mukayi aure, mun kuma samu fahimta wadda take babu yadda za’ayi wata matsala ta kunno kai, domin kuwa munyi kokari wajen magance duk wasu rashin fahimta a tsakani kamin auren mu.

Munyi soyayar nesa a lokacin karatun mu na jami’a, amma abun da yasa soayyar mu tayi karko, ba wani abu bane illa yada muka sa gaskiya da amana a ciki. Mukan samu rashin jituwa amma mukan kokarta mu magance wanna a tsakaninmu kamin wani ya jimu. Don ta haka ne kawai matasa zasu ci gajiyar zama tare. Wanna wata shawara ce daga wasu ma’aurata, kuma a gaba zakuji wasu dalilai goma sha biyu da suke sirin soyayya.