Sabon Robot Yayi Tafiyar Kilomita 400 A Sararin Samaniya

Controls Robot

Wasu masu bincike a kasar Nethrlands, sun kir-kiri wani mashin mai kamar Robot, sun sa mishi kemara da wasu sauran abubuwan kimiyya da fasaha na zamani, sun harba shi cikin sararin samaniya, wanda yayi tafiyar kilomi dari hudu 400, yana yawo cikin sararin samaniya, su kuwa suna nan cikin wannan duniya suna juyashi ta ko’ina.

Wannan wani yunkuri ne da suka kwashe shekaru suna wannan bin ciken, shin wai ta ya, yakamata su gudanar da wannan aikin, a lokacin da suka samu wannan mashin din yayi wannan yawon, sun yi mamaki matuka. A wajen hada wannan mashin din sun kashe kudi kimanin dallar Amurka dubu dari biyu da ashirin da hudu $224,000 kwatan kwacin naira milliyan hamsin kenan 50M.

A cewar su, yawon da wannan robot din yayi a sararin samaniya, bashi ne abu mafi mahinmanci gare su ba, abu mafi mahimanci a nan shine, ace sune sukaje wannan sararin samaniyar, don haka yanzu kokarin su shine suga yadda za’ayi su je da kan su don ganin yadda tsarin duniyar take.