Suna lakani ne da ake ba ma mutun, ko wani abu don bayyanar da shi da kuma hanyar danganta wani abu da wani. Mafi akasarin mutane akan kira su da sunan da iyayen su suka samu su tun lokacin haihuwar su, wanda kuma wannan sunan kan bisu har bayan rayuwar su.
Bisa ga wannan dalilin iyaye kan dauki lokaci wajen zaba ma ‘yayan su suna, wadannda suke da alaka da wasu mutane masu tarihi mai kyau, domin a wasu al’adu ko wasu kabilu, suna da yakinnin cewar idan aka sa ma yaro ko yarinya sunan wani wanda yake mutumin arziki, to ana sa ran wannan yaron ko yarinya idan sun girma suyi koyi da wannan masu asalin sunan da suka gada.
A wasu lokutta kuma akan sama yara suna don kada a manta da sunan wani a cikin dangi. A nan kasar Amurka, wasu sunaye da akayi bincike a ka gano cewar wadannan sunayen sun bace, a cewar hukumar tara bayanan, 'yan-kasa ta nan Amurka, kusan tun shekaru talatin da suka wuce, mafi akasarin iyaye basa sama ‘yayan su wadannan sunayen. Amma ko me nene dalilin hakan? Wadanna sunayen sun hada da, Sophie, Violet, Ella, Lily, Lucy, Stella, Sadie, Oliver, Max, da dai makama mantan hakan.
Abun lura dashi a nan shine, wai da gaske ne idan aka sama yaro ko yarinya sunan wasu magabata, wai wannan yaran kan gado wannan magabatan? Kana wadanne sunananki ne suka bace a cikin naku sunanankin na al’adun ku?