Hadda Su Kaza A Sa Lalle

Amarya da kawayen ta Christine Quinn

Bisa ga al’ada ta kowa ce kabila, yanki, kasa, a duk duniya, a lokacin aure, amarya kan zabo cikin manyan kawayen ta, kannai da dangi don taya ta murna a ranar bukin ta, musamman a wajen zama da abokan mijin. Mafi akasari za’aga cewar amaryar da kawayen ta suna da kusan yawan shekarun haihuwa daya.

Amma abun mamaki a wani gari mai tsawon tarihi a tarihin kasar Amurka, wato Philedelphia, an samu wata amarya mai suna Christine Quinn, wadda ta zabo kakar ta Nana Betty, mai shekaru tamanin da tara 89, a matsayin babbar kawarta a ranar bukin ta.

A tabakin amaryar, "gaskiya na zabo kaka ta ce ta zama cikin manyan kawaye na, domin kuwa ita ce babbar kawata. Ba ko don komai ba sai dan irin yadda take da tunani da sanin yakamata, musamman ma akan abun da ya shafi rayuwa. Domin kuwa a har kullum ina sha’awar ta, kuma ina so nazama kamar ta idan na girma.