Yarda Da Gazawa Ke Haifar Da Mutuwar Zuci

A wasu lokkutta, mutane kan zamo masu kaifin tunani da basira, kana su kan yi nasara a duk abun da suka sa kan su ciki. Har ma za’a dinga kiran su masu farar kafa.

Komai za’aga yana tafiya dai-dai, amma daga lokacin da aka ce jarabawa tazo kan su, wanda za su fara fukantar wasu matsaloli a wannan abun da suke ta samun nasara akai. Daga dai-dai wannan lokacin, sai kaga tunani ya canza baki daya.

Amma abun lura da shi a nan shine, ita gazawa ba itace karshen rayuwa ba, ko ace itace karshen nasarar mutun a rayuwa. Ita gazawa tana nufin cewar, mutun na kan hanya ma dai-dai ciya, wadda mafi yawan mutane da suka zama wani abu a rayuwa, sai da suka fuskanci fadi tashi kamin zama hakan.

Idan za'a duba tarihin mutanen da suka zama wani abu a duniya, za'a ga cewar wadannan mutane sun fukanci wasu gazawa da dama a cikin neman da sukayi har suka kai ma matsayin da suke.

Don haka akwai bukatar matasa su dauki duk wata jarabawa, da tazo musu da manufa mai kyau, da kokarin jajir cewa don ganin sunyi nasara a gaba.