Canjin Yanayi Na Tattare Da Masifu Da Dama

weather

Sai an tashi cikin gaggawa don yaki da cututuka masu yawo a tsakanin mutane. A wani bincike da aka gudanar a jami’ar Arizona ta kasar Amurka, an gano cewar shekarun 2014 da 2015, su ne shekaru da aka samu matsanannciyar cutar sanyi da mura, a duniya fiye da sauran shekaru.

Abu da yakamata mutane su maida hankali a kai shine, dazarar aka ce mutun bashi da lafiya, to kamata yayi mutane da suke kusa da shi, su dauki matakai so sai don guje ma daukar cutar. Domin kuwa an gano cewar, idan mai wata cuta ya rike wani abu kamar ma budin kofa ko ya taba wani abu, da wani shima yazo ya taba, to akwai tabbacin cewar wani kan iya kamuwa da irin wannan cutar, harma yakan iya fin mai asalin cutar zama cikin wahala.

Su dai wadannan kwayoyin cutar da ke yada cututtuka, suna da rai, don haka yake da matukar muhimanci mutane, su dinga wanke hannun su a kowane lokaci, kafun ko bayan shiga taron jama’a. Kuma iyaye su ko karta wajen wanke hannun ‘yayan su. Babban muhimmin abu shine idan mutun bashi da lafiya ko yana jin kasala, to ya nisanta kan shi da jama’a, ko kuwa a ma’aikata su hanzar ta ba marasa lafiya hutu, don guje ma yada cutar ga sauran ma’aikata da al’uma baki daya.