WASHINGTON DC, —
An haifi wasu ‘yan uku masu mugun kama da juna, wadannan jariran basu da wani abu da za’a iya amfani dashi don banbanta su. A cewar likitocin da suka karbi haihuwar yaran, sun ce babu wata alama da take nuna banbanci a tsakanin yaran uku.
Likitocin dai sun samu kuskure wajen sakama yaran lamba, a sanadiyyar haka yasa baza’a iya gane wanene yafito a farko ba, balle na biyu ko kuma na uku. A tabakin iyayen yaran, basu ji dadi ba domin kuwa zasu so, su san wanene ya fara zuwa.
Ita dai uwar yaran ta nuna rashin jin dadin ta domin kuwa tace, ta kwashe kwanaki sama da hamsin 50, a gadon asibiti, don haka gaskiya wannan ya sa bata ji dadin yadda likitocin suka riki haihuwar ba.