Kimiyya da fasaha na kara daukar wani salo a zamanin da ake ciki. Kamfanoni a wannan karnin na kokarin samar da wasu abubuwan kimiyya da basu da makura ko abun kushewa. Duk dai da cewar kimiyya na fuskantar wasu kalubale a wannan karnin.
Kamfanoni masu kera motoci, sun fito da wani sabon tsari na samar da yanar gizo a motoci, a kowane lokaci da wuri, wannan tsarin na bama mutun dammar amfani da yanar gizo koda kuwa mutun na cikin kungurmin daji. Kana mutun kanyi amfani da sabuwar kimiyyar wajen jagoranci zuwa guri, abun da kawai mutun kan bukata shine yasa adireshin inda yake son zuwa.
Ita dai na’urar zata kai mutun duk inda ya samata, ta kuma bayyana ma mutun mintoci nawa yake bukata, don kaiwa gari ko wuri da yake bukatar zuwa. Idan aka samu hatsari a gaba kan hanyar da mutun ke bi, na’urar zata gayama mutun cewar akwai hatsari a gaba, don haka mutun ya tafi sannu a hankali.