A wani bincike da aka gudanar, an iya gano cewar akwai gidajen cin abinci wato “Restaurant” a turance, guda tara 9, da sukafi kowannen dadewa a duniya. Na farko shine “Salzburg” a kasar Austria, wanda aka samar da shi a shekarar 803, kimanin dubban shekaru kenan.
Na biyu kuwa “Zum Franziskaner” na kasar Sweden, shima an samar da shi a shekarun 1421, sai dai a wannan zamanin, anyi mishi wata karamar kwaskwarima wanda gaban shi, yake kama da ginin karni na 20. Amma duk sauran bangarorin suna kama da na wanccan zamanin.
Na uku “La Tour D’Argent” na kasar Paris, France, mai shekaru tun 1500, shima shekarun 1919 ya dan samu wasu kananan canje-canje. Kana na hudu shine “Die Letzten Instanz” na kasar Germany, an kuma samar da shi tun shekarun 1621, wanda a wannan lokacin, sai wane da wane kawai ke iya zuwa cin abinci a wurin.
Na biyar “Sobrino De Botin” na kasar Spain, wanda aka samar da shi a shekarun 1725, anyi shi da katako a wancan zamanin kuma abinci mai tsada a wannan lokacin shine naman Rago da na Alade.
Na shida “Griswold Inn” na jihar Califonia ta Amurka mai shekaru 1776, A wannan shekarun kuwa a cikin mutane masu tarihi sun ci abinci a gidan abincin wanda suka hada da, tsohon shugaban kasar Amurka George Washington, da Albert Einstein.
Na Bakwai “Tavare” na kasar Portugal, mai shekaru 1784. Kana na Takwas, “Rules Restaurant” na kasar Ingila, wanda aka samar da shi a shekarun 1798, shima a wancan zamanin, sai ‘yayan sarauta da hamsha kan masu kudi ka wai ke iya zuwa don cin abinci. Na tara shine “Union Oyster House” na cikin garin Boston a jihar Massachusetts, wanda shine na farko a kasar Amurka.