Amarya Da Gwanjon Kaya Masu Shekaru 120

Amarya Abigail Kingston

Bisa ga al’ada babu amaryar da zata saka kayan da yayar ta tasaka, a ranar daurin auren ta, don cin amarci, balle ma har ace amarya ta saka kayan da mahaifiyar ta tayi amarci da su. Abigail Kingston, zata kafa tarihi, domin kuwa ta shirya saka kayan da kakar ta, ta goma tasa a ranar bikin auren ta. Mutane goma 10, ne suka saka kayan a ranakun bukin su, yanzu ita wannan amaryar itace zata zama ta goma sha daya 11.

Yadda tarihi ya nuna kakka-kakkar Abigail, mai suna Mary Lowry Warren, itace mace ta farko da ta fara saka wannan kayan a ranar daurin auren ta, a ranar 11 ga watan Disamba, shekarar 1895, kimanin shekaru dari da ashirin 120, ke nan. Abun sha’awa a nan shine kowace tasa kayan sai ta ajiye idan ‘yar ta zatayi aure sai ta bata ta sa, a karshe dai an saka kayan a shekarar 1991.

Duk tsawon wannan shekarun sau daya aka taba wanke wannan kayan, kuma tela yayi wani karamin dinkin filawar da ke jikin kayan a karon farko. Ita dai amarya Kingston, tana zaune ne a wani gari mai suna Bethlehem, a jihar Pennsylvania, ta Amurka, ta shirya saka wannan rigar a ranar bukin ta dake tafe, ranar goma sha bakwai 17, na watan Oktoba mai zuwa. Duk dai da cewar kayan sun fita hayyacin su, amma dai tace zata saka su domin tarihi.