Lafiya uwar jiki, babu mai fushi da ita! Masana na ganin cewar akwai bukatar mutane su san me suke ci ako wane lokaci, da kuma daukar matakai da suka kamata wajen tsaftace irin abincin da suke ci.
Sau da yawa mutane kan samu ciwon kai, wanda basu san sanadin hakan ba. Wata mata mai suna Yadira Rostro, tana zama a jihar Texas ta Amurka, ta tafi asibiti don ganin likita, dangane da wani matsanancin ciwon kai da ke damunta. Bayan gudanar da bincike da likita yayi, ya gano cewar tana da wata Tsutsa mai suna ‘Tapeworm’ a turance, a cikin kanta, wadannan tsutsotsin ne ke samata ciwon kai.
A cewar ta, wasu lokutta har bata gani saboda matsanancin ciwon kan, likitocin sun bayyanar da cewar, sanadiyar wadannan tsutsotsin sun shiga kwakwalwar ta shine, a lokacin da tayi tafiya zuwa kasar Mexico, shekaru biyu da suka wuce, taci wani abinci da ya lalace, a sanadiyar haka wadannan tsutsotsin suka shiga cikin jikin ta. An dai samu nasarar ciro tsutsotsin takwas 8, a cikin kwakwalwar ta. Don haka akwai bukatar mutane su dinga kula da irin abincin da suke ci, don kare lafiyar jikin su.