Kare Yasamu Girmamawa A Wajen Jana'iza

A jihar Washington ta Amurka, dubun-dubatan mutane tare da jami’an ‘yan-sanda, sun hadu don karrama wani kare. Shi dai Karen mai suna Ike, an sare shine a lokacin da ake rike dashi a bakin aiki, yayi jinya kamin ya mutu. An bayyanar da karen a matsayin kare da ya taimaka wajen rage yawan aikin ta'addanci a yankin.

Dubun dubatan mutane daga cikin kasar Amurka da makociyar ta kasar Canada, sun halarci jana’izar Karen, wanda suka bayyyanar da kare a matsayin, kare mai kokari wajen gano wasu abubuwa da suka karya doka, da mutane kan boye, kamar su garin wiwi, hodar ibilis, da dai makamantan su. Karen dai ya bada gudunmawa da dama wajen gano masu laifi, a cikin haka ne ma wani mutun mai laifi ya soka ma Karen wuka har sau da dama.

Karen dai yasamu lambar yabo masu yawa, a lokacin jana’izar Karen mutane sun bada gudunwar kudi, don karrama Karen, an birne Karen a bayan gidan shugaban shi, wanda matar mutumin da ‘yayan shi biyu suka tallafa wajen birne Karen.