Gizo-Gizo Yayi Sanadiyar Shiga Kotu A Ingila

Gizo-gizo

Wani lauya mai zaman kansa a kasar Ingila, Mr. John Hogg, ya shigar da karar kamfanin jirgin “Qatar Airline” na kasashen larabawa. Dalilin shi kuwa shine, a lokacin da yake cikin jirgin daga kasar Afrika ta kudu zuwa kasar Birtaniya, wani Gizo-gizo ya cije shi, wanda ya kusa yin sanadiyar rabushi da kafar sa.

Yace a lokacin da suke cikin jirgin, yaga gizo-gizon, wanda wasu mutane sukayi ta ihu cewar ga gizo-gizo, a wannan lokacin gizo-gizon ya fito daga kasan kujerar shi, amma a wannan lokacin baiji wani cizo mai zafi ba, sai bayan kwana daya kafar shi ta kumbura kamar ba tashi ba.

Da ganin haka ya garzaya asibiti inda akayi mishi aiki a kafar sau uku, kuma ya ga likitan fata, likitocin sun gaya mishi cewar kadan ya rage da ko yarasa kafar ko kuma ya mutu, saboda tsanananin dafin wannan cizon gizo-gizon. Yanzu dai yana bukatar kamfanin jirgin, su biyashi duk kudaden daya kashe a sanadiyar cizon gizo-gizon, domin kuwa da sun dauki lafiyar fasinjojin su da muhimanci, da sun tabbatar da magance duk wata hallita da zata cutar da mutane kafin shiga jirgin.