Ba'Amerikiya Ta zabi Zama 'Yar-Najeriya Akan Amurka!

Tambra Raye Stevenson

Da Allah yayi ni ‘yar-Najeriya da nafi jin dadi, Tambra Raye Stevenson, wata ba’amurkiya ce wadda ta bayyana cewar ita baturiyar Amurka ce, amma a gaskiya tafi so ace mata ‘yar-Najeriya. Dalili kuwa shine ta lura da cewar babu abun da Allah, bai yi ma mutanen Najeriya ba, sai dai ace rashin godiya irin ta dan’adam.

Tace an haifeta a jihar Oklahoma, ta kasar Amurka, kuma tayi karatun ta na firamari har zuwa jami’a, a cikin kasar Amurka, wanda yanzu ta kammala karatun digiri na biyu, wato “Masters degree” a fannin abinci mai gina jiki. A cikin bincike da tayi, ta iya gano cewar kasa irin ta Najeriya, tana da duk wasu abubuwa da ba kowace kasa ke da shiba a duniya, musamman na mutane masu basira, da arzikin kasa. Sai ta kara da cewar, har yaushe za’ace wai matasa a Najeriya, basu da aikin yi? wanda yakamata ace matasa su koma gona, don amfani da irin basirar da Allah, yayi musu, ba kawai ace matasa su zauna sai sunyi aiki ofis ba, sau da dama matasa da sukayi aikin gona, su kan fi masu aikin ofis amfani ga kasa.

Ta kara da cewar, da kace matasan Najeriya, zasu zauna suyi amfani da arzikin da Allah, yayi ma kasar su, to da sai dai ace turawan kasar Amurka, su dinga kokawar zuwa kasar Najeriya, don neman aiki da samun abun duniya. Domin gaskiya, kasar Amurka batafi kasar Najeriya, komai ba, kawai abun da zatace kasar Amurka, tafi kasar Najeriya, shine, yadda matasa a nan kasar Amurka, ke kokarin neman na kan su tun bayan sun kammala karatun sakandire wanda bahaka abun yake a kasar Najeriya ba.

Ku biyo mu gobe don jin karshen tattaunawar mu da Tambra. Me nene ra'ayinku dangane da maganar Tambra? Ku rubuto muna a shafin mu na dandalinVOAfacebook.