Kifi "Shark" Ya Maida Wani Musaki

TV-Big Shark

Wani matashi Colin Cook, mai kimanin shekaru ashirin da biyar 25, ya gamu da sanadin rabuwa da kafar shi, a lokacin da suke wasa cikin wani teku a jihar Hawaii ta kasar Amurka, wani katon kifi wanda ake kira “Shark” a turance, ya kaimai hari, wanda hakan yasa likitoci suka ce babu abun da za’a iyayi sai dai a cire kafar, domin kuwa kifin yayi mishi lahani a kafar.

Ya kuma samu rauni a hannun shi, a sanadiyar wani duka da ya kaima kifin. A cewar wani dan’uwan shi, Chris Webster, yace a lokacin da Cook, yayi kokarin guduwa daga inda kifin yake, donceton ranshi zuwa gabar tekun, hakan bai samu ba, domin kuwa kifin ya bishi wanda ya raunata shi.

Ya kuma kara da cewar, likitoci sun bada shawarar a yanke daga gwiwar kafar shit a hagu. Amma yanzu haka yana samun sauki. Wani abokin shi John Carper, shi yayi kokarin fitar dashi daga cikin ruwan.