Kowa a wajen aikin shi Uba ne ko Uwa ce ! Wata mata mai suna Amanda Osbon, tana da yaro karami, kuma tana karatu a jami’ar DeVry, ta garin Nashville jihar Teennesee, a nan kasar Amurka. Tace tana karatun nan ne don ta samarma danta yaruwa tagari. Domin kuwa bata tare da mijinta.
Wata rana tanemi wanda zai rike mata yaron ta, har taje makaranta ta dawo, amma bata samu ba, don haka sai ta yanke shawarar ta tafi da shi aji. Ana cikin gabatar da darasi, sai yaron yayi tsalle yatafi wajen Farfesan dake koyar da ajin, isar yaron wajen farfesan ke da wuya sai Farfesan ya dauke shi. Ya kuma cigaba da rike yaron har aka gama aji.
A tabakin Farfesan, ai yaro dan kowa ne, kuma a hali na rayuwa kowa kan iyasamun kanshi cikin wasu halaye, da ba zai iya magance wasu abubuwa ba. Don haka yakamata kowa ya zama mai taimakon kowa, a duk halin da mutun ya samu kan shi. Ita kuwa uwar yaron tace, gaskiya daga farko taji kunya, don bata taba tsanmanin cewar Farfesa zai iya kula yaron ta ba. Amma sai gashi har yana nuna cewar yasan irin wannan halin, a rayuwa da kuma bamu shawarar mu dinga taimakama juna. Hakan yasa gaskiya naji dadi matuka.