Shin Yanar Gizo Zata Haifar Ma Duniya Alkhairi Kuwa?

Internet Dating

A wani bincike da aka gudanar dake nuni da cewar, bada dadewa ba nan da shekarar 2022, rashin aikinyi zai iya karuwa da wasu kaso masu yawa, bisa wasu dalilai. Masu binciken sun mika lambar yabo da jinjina ga kafofin sadarwa na email, Facebook, Twitter, da dai sauran shafufukan sadarwa na yanar gizo.

A cewar hukumar neman aiki da tantancewa ta kasar Amurka, a shekarar 2022 za’a samu matsalar rashin aikinyi musamman ga ma’aikatan “Gidan Waya” wato masu kai sako gida-gida ko ma’aikata-ma’aikata, kamar su NIPOST, DHL, FEDEX, da dai makamantan su. Dalili kuwa shine yadda yanar gizo ta saukaka abubuwa da dama. Amma hakan kan iya zamowa illa babba, domin kuwa za’a rasa aikin yi kana, sace-sacen bayanai zai kara karfi a duniya.

Haka kuma sauran ayyuka da zasu jawo karin rashin aikin yi, sun hada da aikin buga jarida, katutuka, kalanda, da dai ire-iren su. Masu sana’ar saida kifi, masu zanen kwamfuta, domin kuwa yanzu ana sama kwamfutoci wasu sinadarai da kowa zai iya aiki dasu ta yadda yake so, haka suma masu aikin gidan wuta, da ma’aikatan jirgi. Domin kuwa yanzu ana kara cigaba da kirkirar mutun-mutumi “Robot” a duniya, wanda ake da tsammanin cewar zai maye gurbin mutane a wajen ayyuka da dama.