Takobi Dan Shekaru 1,200 Ya Sake Bayyana

Takobi

Wani mutun mai suna “Goran Olsen” dan karamar hukumar “Hordaland” ta kasar “Norway” yana kan hanyar shi ta zuwa wajen wasa cikin teku, sai ya tsaya don ya huta a tsakanin wasu duwatsu, yana dubawa karkashin wani gungumemen dutse sai ya ga wani “Takobi” an dai kiyasta shekarun wannan takobi da cewar zai kai shekaru dubu daya da dari biyu 1,200. A cewar masu binciken arzikin cikin karkashin kasa.

Wannan takobin yana iya yuwa takobin wani ne ya fadi tun a wancan lokacin, haka kuma wannan takobin bai yi komai ba, sai dai kawai yayi baki. Sun ce gaskiya wannan abun ban’al’ajabi ne don ba’a cika samun irin wannan abubuwan ba.

Mr. Per Morten Ekerhovd, shugaban gidan ajiye kayan tarihi na kasar, ya bayyanama manema labarai cewar, lallai wannan takobin za’a iya amfani dashi idan anaso a wannan zamanin. Abu kawai da ake bukata shine a goge shi, kuma ayi mishi hannu. Don tsawon takobin yayi dai-dai da yadda ake bukatar takobi. An dai bayyanar da cewar takobin na iya yin wadannan shekarun, a dalilin irin yanayi da ake dashi a kasar na dusar kankara.