Ranar Daukaka Darajar Kabewa "Goji" A Kasar Amurka

A irin al’ada ta kasar Amurka, a kowace shekara ranar 30 ga watan Oktoba, akanyi wani buki da ake kira “Halloween” shi dai wannan buki bias ga al’ada buki da ake yi wanda mutane zasu hadu a waje don mutnar zagayowar wannan ranar. A kasar Amurka, daga kawai ance Halloween, abun da kawai zaizo tunanin mutane shine Kabewa. Domin kuwa an alakanta wannan bukin da ita "Goji" wato Kabewa.

Akanyi “Party” don murnar wannan ranar, kuma iyalai kan girka abinci mafi dadi don ci a tsakanin iyalai da masoya. Haka kuma shi wannan bukin gayara shine buki da sukafi so a duk cikin bukukuwa da ake dasu a Amurka, dalili kuwa shine, buki ne da ake ba yara Alawa, su cakulet, minti, da dai dangin kayan zaki.

Haka kuma yaran kansa kaya na wasu dabbobi ko wasu abubuwa masu ban tsaoro, kamar su fatalwa, namun daji, da dai makaman tansu. Wannan bukin ya samo asali ne da cewar rana ce da matattu ke tasowa daga cikin kabarin su. Don haka iyalai su kanje gidajen gona da ake kayatar dasu da wasu abubuwan ban-tsoro da yara don gani da annashuwa.