An bayanar da wasu garuruwa a matsayin garuruwan da sukafi kowannen kyau a fadin duniya. Akwai abubuwa da dama da aka lura dasu wajen zaben wadannan garuruwa. An duba yadda tsarin garuruwan suke, da yadda mu’amalar mutanen garin suke ga baki, kana da al’adun garin, siyasar garin, harma da irin cigaba da aka samu a garin bayan wasu shekaru.
Garin “Stockhlm” na kasar Sweden shine gari na farko da yafi kowane gari kyau a duniya, sai garin “Dresden” na kasar Germany, shi dai wannan garin an wargaza shi a lokacin yakin duniya na biyu, amma a zuwa yanzu an sake gina shi kuma yana daga cikin garuruwa masu kyau. Sai garin “Shanghai” na kasar China, daga nan sai garin “Dublin” na kasar Irelan, sai garin “Hong Kong” na kasar China shima, haka kuma garin “Singapore” yana daya daga cikin su.
Garin da ya biyo bayan su shine garin “Victoria” na kasar Canada, sai “Quebec City” duk a cikin kasar Canada. Na gaba kuwa shine garin “Madrid” na kasar Spain, sai garin “Siena” na kasar Italy, garin “Edinburgh” na kasar Scotland shima ba'a bar shi a baya ba. Sai garin “Vancouver” na kasar Canada, sai garin “Lucerne” na kasar Swetzelan, haka garin “Amsterdam” na kasar Netherlands shima yana daga cikin garuruwa masu kyau a duniya.