Garuruwa Masu Tsare-Tsare Fiye Da Saura A Fadin Duniya

Sauran garuruwa da su kafi kyau a fadin duniya sun hada da gari na farko a yankin kasashen Afrika shine garin “Cape Town” wato babban birnin tarayyar kasar Afrika ta kudu, sai “Tokyo” ta kasar Japan, da “Barcelona” na kasar Spain, sai garin “Venice” na kasar Italy, kana da garin “Salzburg” na kasar Austria, sai garin “Jerusalem” na kasar Israel.

Sauran sun hada da garin “London” na kasar Ingila, da garin “Kyoto” na kasar Japan, haka ma garin “Bruges” na kasar Belgiu, da garin “Prague” na kasar Czech Republic, da garin “Rome” na kasar Italy, sai garin “Paris” na kasar France, haka ma garin “Sydney” na kasar Australia, da garin “Vienna” duk a kasar ta Australia, haka garin “Budapest” na kasar Hungary, kana na karshe a wannan tsarin shine garin “Florence” na kasar Italy.

Duk da irin yawan kudade da ake kashewa wajen gine gine da tsar-tsare a kasashen Afrik, da kasashen yankin larabawa babu garin da ya shiga cikin tsarin, kasashen da sukafi kyau a duniya. Munaso muji ra’ayoyin ku dangane da hakan.