Moshe Kai Cavalin, dan shekaru goma-sha bakwai 17, yazama daya daga cikin dubu, da suka samu cinma wasu nasarori a rayuwa. Yanzu haka dai ya kammala digiri guda biyu, daga jami’ar California, kuma marubucin littatafai ne haka kuma matukin jirgin sama ne.
Yana ganin cewar shekarun sun kawo mishi cikasa, domin kuwa da shekaru 17 bashi da damar da zai tuka mota shi kadai, amma yana tuka jirgin sama, yanzu haka dai ya kamala rubuta littatafai guda biyu. Yana kuma aiki da hukumar binciken sararin samaniya NASA, inda yake cikin wani ayari masu aiki, da ake kokarin samar da wata sabuwar na’ura mai ganin jirage da “Drone” a sararin samaniya.
Ya bayyanar da kan shi a matsayin wani yaro na daban, wanda yake ganin cewar wannan irin basira da Allah, yayi mishi tana da nasaba da asalin shi, domin kuwa baban shi dan asalin kasar Brazil ne ita kuwa mahaifiyar shi ‘yar kasar Taiwan ce. Yana ganin hakan shiya sa yazama mai hazaka. Wanda yace wannan basirar tashi kowa na iya samun ta, babu ma kamar akace yara masu kananan shekaru, zasu dinga mayincewa a wajen karanta abubuwa, da kuma tambayar yaya akayi wajen kirkirar wadannan abubuwan.