Yaro Dan Shekaru 10 Ya Roki Alkali Da Ya Kulle Maman Shi A Kurkuku

baby

Bradyn Smith, mai shekatu goma 10, ya rubuta ma alkali wasika da cewar kada alkali ya saki mahaifiyar shi daga gidan yari. Ya gayama alkali cewar a shekarar 2009 lokacin da yake dan shekaru 4, wata rana baban shi da maman shi suna fada, yagani da idon shi lokacin da maman shi ta dauki wuka ta daba ma baban shi a wuya, wanda hakan yayi sanadiyar mutuwan uban shi.

Yana ganin cewar bai kamata a saketa ba, domin kuwa idan da bata kashe mishi baba ba, da yanzu rayuwa tazama sau dubu fiye da yadda yake a yanzu. Alkalin ya daukar ma uwar yaron wa’adin karin shekara daya a gidan kasu, har zuwa karshen shekara mai zuwa, dai-dai da tayi shekaru 7. Bayan nan zata koma gida tayi shekaru uku 3, a cikin gida ba fita. Lauya mai kare uwar, yayi godiya da sassaucin alkalin, wanda yace hakan zai iya zama wata dama da zata koma don ta dai-daita tsakanin ta da ‘yayanta biyu.