Wani Uba Ya Bada Dan Shi Kyauta Ba Dalili

Wani yaro da ya bace kimanin shekaru goma sha uku 13, ya sake bayyana. Julian, ya bace tun yana dan shekaru biyar 5, tun bayan bacewar yaron an neme shi amma ba’a ganshi ba, har takaiga iyayen yaron sun hakura. Rana tsaka sai ga yaron ya kamala karatun sakandire zai shiga jami’a, a wannan lokacin an saka labar tashi ta “Social Security” sai ta nuna wani suna na daban, daga nan sai suka fara tambayan yaron, ya’akayi sunan da ya bada ya banbanta da wanda ke rubuce a runbun ajiye baya nai na kasa baki daya.

Abun al’ajabi shima yaron bai san da cewar ashe sace shi akayi ba, don haka sai ya sake tambayar hukumomin makarantar da cewar akwai wata matsala, sai suka gaya mishi cewar sunan shi da lambar shi basu yi dai-dai ba, daga nan sai aka sanar da hukumomin jami’an binciken manya laifufuka ta kasa wato “FBI” koda aka zurfafa bincike sai aka gano cewar iyayen yaron suna wani gari, wanda ke da nisan kiman mil dari bakwai 700, daga gidan da aka rene shi ya kuma dauka cewar sune iyayen shi na asali.

A dai-dai lokacin da aka kira mahaifiyar yaron da cewar anga yaron ta bayan shekaru 13, Julian Hernandez sai tace “Da gaske? Kun tabbata shine kuwa? Da gaske kuwa?” Bayan zurfafa bincike sai aka gano cewar ashe mahaifin yaron ne ya bada yaron tun a wancan lokacin. Zuwa yanzu dai ba’a san dalilin da yasa uban yaron yayi hakaba amma dai ana cigaba da gudanar da bincike.