Karyar Satar Kama Ta Kare A Kasashen Da Suka Ci Gaba

A tsari irin na kasashe da suka cigaba, kamar kasar Amurka, suna da wani tsari wanda idan aka haifi jarirai, mintoci kadan bayan fitowar su daga cikin mahaifiyar su, za’a dauki samfurin kafar su da na hannun su, daga nan za’a basu takardar shaidar haihuwa, kana abasu wata lanba da ake danganta ta da kowane dan-kasa. Duk wannan bayanan na mutun zai shiga cikin runbun bayanai na 'yan kasa har bayan rayuwar dan-kasa.

Ita dai wannan lambar da ake kira “Social Security” ta kowa ta banbanta da ta wani, ita dai wannan lambar mutun zai dinga amfani da ita akowane abu zaiyi a iya tsawon rayuwar shi a kasar. Idan mutun yayi wani laifi za’a danganta laifin shi da wannan lambar. Wanda idan mutun ya tafi neman aiki za’a saka wannan lambar don ganin tarihin rayuwar shi. Idan an same shi da wani laifi da zai sa ba za’a bashi aiki ba, za'a sanar dashi dalili, don haka a duk lokutta mutane suna kiyaye wannan lambar.

A sanadiyar wannan lambar da ake ba kowane dan kasa, za’a iya gane mutun nawa aka haifa a rana, kuma mutun nawa suka mutu a rana, a daukacin kasar baki daya. Haka ma baki da suka shigo kasar don zama na wani tsawon lokaci, ta hanyar da ta dace, akan basu wannan lambar, domin a san irin kai-kawo da sukayi a cikin kasar, sai dai tasu takan banbanta da ta ‘yan kasa. Wannan wani tsari ne da zai baiwa gwamnati da kamfanoni damar sanin mutun, da kuma irin gudun mawa da yake badawa a wajen gina kasa. Duk kuma dan-kasa da ke aiki ko 'yan-kasuwa sukan bada wasu gudun mawa na kudi ga wannan tsarin, wanda idan mutun ya tsufa ko ya bar aiki za'a dinga tallafa mishi har ya mutu.