Wasu Abubuwa Da Matasa Kan Aikata Ba Cikin Saniba

Matasa

A wani bincike da aka gudanar dake bayyanar da cewar, akwai wasu abubuwa da mafi akasarin matasa kanyi ba cikin sani ba, a wasu lokutta wanda daga baya mutun yaji kunyar aikata wadannan abubuwan. Da dama idan mutun ya duba cikin rayuwar shi zai gazgata yin daya zuwa biyu cikin wadannan abubuwan.

Na farko shine a wasu lokutta mutun kan dinga magana da kanshi batare da ya ankara ba, wanda mutun zai danyi wata karamar tabuwar hankali na wasu kanan lokaci. Wasu lokkuta kuma mutun kanyi wani abun kunya, da zai koma daga baya ya dinga tambayan kanshi wai da gaske nayi wannan abun kuwa?

Sau da dama mutun kan dinga mai-maita labari da ya taba fade, hakan kuma kan ba wasu abokan shi haushi, domin zasu ga ka dame su da labari daya, ko kuma hakan na iya nuna cewar mutun na cikin wata damuwa. Bincike ya nuna cewar sau da dama mutane basu iya tuna ko sun bada wannan labarin ko kuwa, ko kuwa wa suka taba ba labarin?

Haka kuma mutane kan tsinka waya a lokacin da suke magana da wasu, wani lokaci bacikin sanin su ba, kodai cikin bacin rai ko kuma cikin kunya da wasu abubuwa makamantan haka. Ko kuma da yawa matasa kan bar wayar su a ban-daki wato “Toilet” da dama matasa kan shiga ban-daki da wayar su, kodai suna buga game, ko wani abu wanda zasu fito su manta da ita a cikin bayin.

Wanne ka/kika taba yi? Ku rubuto muna a shafin mu na Dandalinvoa/facebook.com